Tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine | Labarai | DW | 09.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tattaunawa tsakanin Rasha da Ukraine

Gwamantin Ukraine da takwararta Rasha sun fara wata tattaunawa kan saidawa Ukraine din iskar gas da kuma kawo karshen rikici a gabashin Ukraine din.

Bangarorin biyu dai na ganawa ne kan wadannan batutuwa a Brussels da Kiev, yayin da a hannu guda ake cigaba da yin dauki ba dadi tsakanin jami'an tsaron Ukraine da 'yan awaren da ke goyon bayan Moscow a birnin nan na Slavyansk har ma rundunar sojin kasar ke cewar an kame mata wasu daga cikin dakarunta.

Wannan yanayi dai na zuwa ne daidai lokacin da shugaban na Ukraine Petro Poroshenko ya yi shelar warware rikicin siyasar Ukraine din cikin mako guda bayan da ya sha rantsuwar kama aiki a ranar Asabar din da ta gabata.

Da dama dai na ganin da wuya a kai ga cimma yarjejeniya kan iskar Gas tsakanin Ukraine da Rasha kasancewar wa'adin da Rasha ta debawa Ukraine na biyanta bashin dala miliyan 4 da rabi da ta ke binta na cinikin gas din da suka yi na dab da cika.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman