Tasirin yajin aikin ma′aikatan mai a tattalin arzikin Najeriya | Siyasa | DW | 10.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tasirin yajin aikin ma'aikatan mai a tattalin arzikin Najeriya

Janye yajin aikin dai na zuwa ne bayan da ministan kasa a ma'aikatar albarkatun na mai Ibe Kachikwu ya bada tabbacin cewa babu batun rasa ayyukan yi a tsakanin ma'aikatan.

Nigeria National Petroleum Corporation Öl-Industrie Korruption

Kamfanin NNPC a Abuja Najeriya

Tsayar da harkoki cik a fanin harkara man fetir din Najeriyar har na fiye da sao’I 24 a kasar babban al’amari ne ga kasa irin Najeriya da fiye da kashi 90 cikin 100 na kudaden shigarata suna fitowa ne daga man fetir, abin da ya sanya lamarin girgiza daukacin al’ammura har ma da wadanda basu shafi man fetir din ba.


Nigeria National Petroleum Corporation Wechsel Konzernspitze

Ministan mai a Najeriya Ibe Kachikwu (a hannun dama)

Jayaya a game da sake fasalin daukacin harkar man Najeriyar da ake wa kallon an maida shi sashin da jami’an gwamnati ke wasoso na kudaden da aka basu amana, abin da ya jefa Najeriyar cikin mummunan hali da take ciki a yanzu duk kuwa da karfin tattalin arzikinta. Malam Abubakar Ali kwararre a fanin tattalin arziki da ci gaban kasa ya bayyana wannan yajin aiki da zama illa duk da janye yajin aikin.


Gwamnatin Najeriyar dai na mai bayyana dalilai na gyara domin samun daidatuwar al’amari ta yadda talaka zai shaida cewa lallai kasarsa na da arzikin mai a matsayin dalilai na kacaccana kamfanin na NNPC ta yadda zai kasance mai bada riba.


Nigeria Tankstelle in Lagos

Dan bumburutu kasuwa ta bude

Tuni dai lamarin ya haifar da karin wahalhalu da matsaloli ga al'ummar Najeriyar musamman ta fanin karancin man da dama can ake fama da shi da kuma ke shafar farashin kayayyaki da karanci na wutar lanatarki. To sai dai wasu na hangen gwamnati na dauka wannan mataki ne da kyakkyawar niyya kamar yadda Alh Usman Ibrahim Gamawa na kungiyoyin matasan Arewa maso Gabashin Najeriya yayi ammanna.


A yayin da gwamnatin ta shawo kan kungiyoyin ma’aikatan kamfanin man na NNPC, al’ummar Najeriya za su sa idon ganin tasiri na zahiri na gaggarumin garambawul da ake yi wa NNPC domin rarabe aya da tsakuwa a kokarin alkinta albakar man da Allah ya hore wa kasar da fiye da shekaru hamsin talakanta ke cewa bai fa kai ga gani a kasa ba.

Sauti da bidiyo akan labarin