1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankula a Iraki sun ki karewa

January 15, 2014

Mutane da yawan gaske aka kashe a jerin hare-haren kunar bakin wake a Iraki a ci-gaba da tashe-tashen hankula tsakanin jami'an tsaro da masu ta da kayar baya.

https://p.dw.com/p/1Aqxt
Hoto: picture alliance/AP Photo

Hukumomin tsaro a Iraki sun ce akalla mutane 46 aka halaka a jerin hare-hare a fadin kasar. A Bagadaza babban birnin kasar motoci bakwai ne da aka dana masu bam suka fashe cikin lokacin kankane. Hari mafi muni ya auku ne a yankin Bohroz dake cikin lardin Dijala dake arewa da Bagadaza, lokacin da wani dan kunar bakin wake ya ta da bam a jikinsa yayin jana'izar wani mai adawa da kungiyar al-Qaida. Likitoci da 'yan sanda sun ce maharin ya hallaka akalla mutane 16. A kuma halin da ake ciki dakarun tsaron kasar na kara samun koma-baya a fadan da ake yi a lardin Anbar dake yammacin kasar. 'Yan Sunni masu ta da kayar baya sun tilasta wa 'yan sanda tashi daga wani gida da suke gadi a wata unguwa dake Ramadi babban birnin lardin na Anbar, sannan suka kwace makamansu.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umar Aliyu