Tashe tashen hankula a Iraki sun halaka akalla mutane 50 | Labarai | DW | 20.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tashe tashen hankula a Iraki sun halaka akalla mutane 50

Sama da mutane 50 suka rasu sannan da dama suka samu raunuka sakamakon jerin hare hare da aka kai a Iraqi a jiya asabar. Akalla mutane 35 suka mutu lokacin da wani dan harin kunar bakin wake ya tuka motarsa dauke da bama-bamai cikin masu jana´iza a kusa da birnin Baquba dake arewa da Bagadaza babban birnin Iraqi. Gabanin wannan harin dai mutane 13 aka kashe a wani harin bam da aka dana cikin wata mota da aka kai kan wata kasuwa dake birnin Bagadaza. An kuma kai wasu hare haren bam guda biyu a arewacin kasar ta Iraqi, inda aka halaka sojin Amirka 5 dake sintiri a kusa da birnin Baiji.