Taron tattaunawar zaman lafiyar Sudan dake gudana a Nigeria ya kare ba tare da cimma manufar da ake bukataba-- | Siyasa | DW | 15.09.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron tattaunawar zaman lafiyar Sudan dake gudana a Nigeria ya kare ba tare da cimma manufar da ake bukataba--

Kungiyaryan tawayen Sudan mai da'awar tabatar da mulki na adalci ta bada sanarwar rushewar taron sulhun Abuja---

default

Mahukuntan kasar Equatorial Guinea sun fara daukar matakai na korar baki daga cikin kasar tun bayan da wasu sojin haya na kasahen ketare suka yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar watani shidan da suka gabata.

Wani dan asalin kasar Ghana mai suna Tony na daya daga cikin bakin haure da jami’an tsaron kasar ta Equatorial Guinea mai arzikin mai suka kama.

Dan asalin kasar dai ta Ghana yana cikin aikin goge gilashi a wata karamar mashaya da ya kafa a baban birnin kasar ta Euatorial Guninea lokacin da yan sanda suka yi awon gaba da shi,aka kuma tsare shi a gidan kurkuku tare da wasu daruruwan bakin haure har ya zuwa tsawon makoni uku kafin kuma a kore su daga cikin wanan karamar kasa mai arzikin mai dake tsakiyar Africa.

Koda yake an kore Tony dan asalin kasar ta Ghana daga Euqatorial Guinea amman kuma ya sake komawa,inda kuma ya baiyana cewar a tsawon shekaru biyu da yayi yana zaune a kasar ya furta cewar duk da wahala ta rayuwa amman kuma ya sami amfani a zamansa na kasar ta Euatorial Guinea.

Bayan kwanaki da yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar Equatorial Guinea da bai ce nasara ba,gwamnatin kasar Ghana ta bada umarnin a kwaso yan kasarta daga cikin wanan kasa,yayin kuma da aka tsare wasu da daman su wasu daruruwan yan asalin kasar ta Ghana suka nemi mafaka a ofishin jakadancin Ghana dake kasar ta Equatrial Guinea.

Bugu da kari ita ma gwamnatin kasar kamaru ta kira jakadanta zuwa gida,bayan da ta koka da cewar jami’an tsaron Equatorial Guinea sun ci zarafin yan kasar ta Kamaru kafin a kore su daga cikin kasar.

Dan asalin kasar ta Ghana da mahukuntan Equatorila Guinea suka kora zuwa gida bayan da gwamnati ta dauki mataki na korar bakin haure daga cikin kasarta,ya koka da cewar bayan shekaru biyu da yayi yana aiki na wahala a kasar Euatorial Guinea,an dauke shine a matsayin baban mai laifi domin a lokacin da aka kore shi zuwa kasarsa ta haihuwa Ghana ba tare da kudade ko abinda ya malaka ba illa suturar dake jikinsa a tabakin Tony dan asalin kasar ta Ghana.

A lokacin da ya sake komawa Malabo baban birnin kasar ta Euatorial Guinea ya sami taimako ne daga yan uwansa,kuma a lokacin da ya koma din babu wani abu da ya samu daga cikin irin abinda ya malaka.

Dan asalin kasar ta Ghana ya kara da cewar da dama daga cikin bakin hauren da aka kora daga Equatorial Guinea sun sake komawa kasar,don su sami sukunin cigaba da rayuwa a tsohuwar kasar da Spain ta yiwa mulkin malaka.

Da dama daga cikin bakin hauren da suka koma kasar ta Euatorial Guinea,suna wasan buya ne da jami’an tsaro inda wasun su suka rika buya a tsakanin duwatsu masu amon wuta ko kuma kungurmin daji.

Wata yar asalin kasar Benin Zoubeda mai shekaru 22 da haihuwa dake sana’ar sayar da kayan kwaliya na mata a kasuwar tsakiyar Malabo ta baiyana cewar babu wani batu na kare hakin dan adama a kasar Euatorial Guinea,saboda lokacin da aka kamata ta shafe mako biyu tana tsare duk kuwa da cewar tana da cikakun takardun izinin zaman kasa hasali ma ba’a sameta da aikata wani laifi ba.

An dai baiyana cewar azikin mai da Allah ya horewa kasar Euatorial Guinea na zaman daya daga cikin dalilan da suka janwo hankula duban bakin da suka fito daga kasahen tsakiyar Africa da yammacin Africa zuwa kasar.

 • Kwanan wata 15.09.2004
 • Mawallafi Jam,ilu Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvgT
 • Kwanan wata 15.09.2004
 • Mawallafi Jam,ilu Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvgT