Taron shugabanin Kungiyar Taraiyar Turai | Labarai | DW | 21.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron shugabanin Kungiyar Taraiyar Turai

Shugabanin kasashen turai sun hallara a birnin Brussels inda zasu tattauna kann sabuwar yarjejeniya da nufin kawo gyare gyare cikin harkokin KTT.Manyan batutuwa cikin yarjejeniyar sun janyo muhawara mai zafi inda kasashen Poland da Burtaniya sukayi barazanar darewa kujerar naki muddin dai baa magance batutuwa da suka mika gaban taron ba.

Poland dai tayi suka da kakkusar murya wani tsarin jefa kuria da Jamus ta shawarta a bi tana mai cewa manyan kasashe ne kadai zasu ci moriyarsa.

Firaministan Luxemburg Jean-Claude Junc yace muddin dai baa cimma yarjejeniya a taron ba yana nufin cewa baza sake daukar sabbin membobi cikin kungiyar ba.

Sabuwar yarjejeniyar ana nufin ta maye gurbin kundin tsarin mulkin kungiyar ne da bai samu karbuwa ba a kasashen faransa da Netherlands.