Taron kungiyar G8 na tattaunawa akan sauyin yanayi | Labarai | DW | 07.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kungiyar G8 na tattaunawa akan sauyin yanayi

Sauran muhimman batutuwa da shugabannin na G8 zasu kuma mayar da hankali kan su a taron na yau sun hada halin da tattalin arzikin duniya ya ke ciki sai yankin Darfur, Kosovo da halin da ake ciki a yankin GTT sai kuma batun sauyin yanayi. Mai masaukin baki SGJ Angela Merkel na son shugabannin manyan kasashe mafiya arzikin masana´antu a duniya da su amince da wata yarjejeniya wadda zata tanadi rage yawan hayaki mai gurbata yanayi kamar yadda yake kunshe a cikin wani kudurin MDD.

To sai dai FM Birtaniya mai barin gado Tony Blair ya ce shugabannin G8 zasu rage fid da gurbataccen hayaki amma ba zasu sanya wani adadi takamamme ba. Shi shugaba Bush ya ce a shirye Amirka ta ke ta za jagora wajen kulla wata yarjejeniya da zata maye gurbin yarjejeniyar Kyoto bayan shekara ta 2012.