Taron kolin kasashen Euromed a Barcelona na kasar Spain | Labarai | DW | 27.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kolin kasashen Euromed a Barcelona na kasar Spain

Shugabannin kasashen Turai da takwarorinsu na yankin tekun bahar Rum sun hallara a birnin Barcelona na kasar Spain don gudanar da wani taron koli irinsa na farko tsakanin yankunan su. An dai shirya taron ne da nufin karfafa huldar dangantaku tsakanin kasashe 25 na tarayyar Turai da kasashe 10 makwbtansu na kudu. To sai dai shugabannin kasashe biyu kadai ne daga cikin kawayensu Larabawa da kuma Isra´ila ke halartar taron kolin. Sabuwar shugabar tarayyar Jamus Angela Merkel zata yi amfani da wannan taron don tattaunawa da FM Turkiya Recep Tayyip Erdogan.