Taron koli na kungiyar EU kan ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 17.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron koli na kungiyar EU kan 'yan gudun hijira

Shugabannin kasashen da ke da kujera a Kungiyar gamayyar Turai za su gudanar da taron koli na musamman a kan matsalar 'yan gudun hijira a mako mai zuwa.

Shugabannin kasashenTurai za su gudanar da wani taro koli na musamman a ranar Laraba mai zuwa a birnin Bruselles, da nufin tinkarar matsalar 'yan gudun hijira mafi muna da nahiyarsu ta fuskanta a cikin shekaru 70 da suka gabata. Shugaban karba-karba na EU Donald Tusk ne ya yi wannan sanarwa a shafinsa na sa da zumunci na Twitter. Wannan taro da Jamus ta matsa lamba domin a gudanar da shi, zai zo ne kwana daya bayan wanda ministocin cikin gida na kasashe EU za su gudanar a kan batun na 'yan gudun hijira.

Shugabanni 28 za su yi kokarin fahimtar juna kan rabon 'yan gudun hijira dubu 120 da suka mamaye kasashen Italiya da Girka da kuma Hangari. Kasashen dai ba su yi nasarar cimma matsaya a kan matsalar ta 'yin gudun hijira ba, a taron da ministocin cikin gida na Turai da suka gudanar a ranar Litinin da ta gabata saboda rarrabuwar kawuna da suke fuskanta a kan wannan batu.