1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nazari kan cigaban harkokin zuba jari a Afirka

Ramatu Garba Baba
November 9, 2018

Masu ruwa da tsaki kan harkokin zuba jari a kasashen Afirka sun fara wani taro na kwanaki uku a birnin Johannesburg da ke Afirka ta Kudu inda taron zai kara yin nazari kan zuba jari da cigaban nahiyar.

https://p.dw.com/p/37xdx
Gipfeltreffen der Brics-Staaten in Südafrika
Hoto: Getty Images/M.Hutchings

Masu shirya taron sun yi masa lakabi da ''hada-hadar zuba jari ta karni a Afirka domin cigaba''. Shugaban bankin raya kasashen Afirka Akinwumi Adesina ya bayyana taron na Johannesburg a matsayin sauyi da zai bada damar zuba jari domin inganta nahiyar Afirka a nan gaba. An cimma matsaya ta kasuwanci guda 61 daga bangarori daban-daban na nahiyar Afirka wanda ta kai kimanin dalar Amirka miliyan dubu arba'in.

Hakan dai ya ja hankalin masu zuba jari har suka fara tofa albarkacin bakin su. A daura da wannan, shugaban lardin Gauteng da ke Afirka ta Kudu David Makhura wanda ke cikin mahalarta wannan zama ya kalubalanci gwamnatocin Afirka da su yi duk mai yiwuwa domin ganin an samu nasarar amfana da damarmakin da aka samar a wannan taron.

Patrick Dlamini da ke jagorantar bankin raya kasa na Afirka ta Kudu ya ce bankuna a shirye suke su samar da kudade domin Afirka ta samu nasara. Ana dai sa ran wannan taro zai taimaka wajen bunkasa harkar tattalin arziki da kuma janyo hankulan masu zuba jari a nahiyar Afirka, nahiyar da wasu ke yi wa kallon koma-baya ta fuskar cigaba a fannoni da daban-daban.