Taron ECOWAS ko CEDEOA karo na 59 a Ghana | Siyasa | DW | 22.06.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Taron ECOWAS ko CEDEOA karo na 59 a Ghana

A karshen makon da ya gabata ne, aka kammala taron shugabannin kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirika ta Yamma wato ECOWAS ko CEDEAO karo na 59 a kasar Ghana.

Ghana Präsident Nana Akufo-Addo mit Maske

Shugaban kungiyar ECOWAS ko CEDEAO kana shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

Taron ya gudan ne karkashin jagorancin shugabanta kana shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo, kuma ya samu halartar shugabannin kasashen yammacin Afirka da dama da suka hadar da Najeriya da Burkina Faso da Cape Verde. Batutuwa da dama ne dai suka kankane tattaunawar taron na shugabannin kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO, inda muhimmi shi ne batun sanya matakan dakile yaduwar cutar COVID-19 da lalubo hanyar kirkirar allurar riga-kafi da samar kwanciyar hankali da tsaro da bunkasar dimukuradiyya a nahiyar da magance matsalar tashe-tashen hankula. Sai kuma batun tattalin arziki da karfafa hulda tsakanin takwarorin ECOWAS da batutuwan kan iyakoki da shugabanci da huldar kasuwancin tsakanin kasashen Afrika AFCFTA.

Karin Bayani: Martanin ECOWAS ko CEDEAO kan Mali 

Sun kuma tattauna batun shugabancin kungiyar na karba-karba da uwa uba batun kudin bai daya na ECO, wanda aka jingine aiwatuwar da shi zuwa shekarar 2027. An dai jima ana samun sabanin tsakanin abokan huldar kasuwanci musamman a Ghana, wanda ke faruwa tsakanin 'yan kasuwa 'yan asalin Najeriya da abokan kasuwancinsu a Ghanan. A ranar  18 ga watan Disambar wannan shekara da muke ciki ne dai, ake saran shugabannin za su kara hallara a Abuja fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya domin gudanar da sabon taro.

Sauti da bidiyo akan labarin