Amfani da takardar kudi ta ECO a yammacin Afirka | BATUTUWA | DW | 21.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Amfani da takardar kudi ta ECO a yammacin Afirka

Faransa ta amince da batun soma amfani da takardar kudin ECO a yankin yammacin Afirka maimakon CFA da aka saba kashewa tare da amincewa da takardar kudin Euro ta zame wa kudin ECO gata wajen Canji.

Batun kudin CFA ya haifar da dimi mai zafin gaske tun bayan da shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na kasar Côte d’Ivoire suka sanar da yunkurin sauya kudin daga CFA zuwa na ECO a ranar 21 ga watan Disamban shekarar da tagabata, Ana ganin kudi ne da kungiyar ECOWAS da kanta ta zabi wannan suna kuma take da niyar samar da kudin na bai daya masu sunan ECO. Sai dai ga alama kasashen yammacin Afirka rainon Faransa masu amfani da kudin CFA ne za su soma da cin wannan gajiya ta soma amfani da kudin ECO kafin sauran takwarorinsu na kasashe bakwai na ECOWAS cikinsu har da su Najeriya da Ghana. 

Masana na sharhi kan kudin ECO 

Taron majalisar ministocin Faransa ya amince da fitar kasashen daga CFA zuwa ECO, lamarin da ya haifar da ra'ayoyi mabanbanta daga masana tattalin arziki, ko da yake wasu masu sharhi kan harkokin siyasar duniya irin su Mamane sani Adamou har yanzu akwai sauran rina ka inda ya ce "muddin ana son samun cikakken 'yanci da walwala ta fannin tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka dole ne ya kasance kasashen ne da kansu ke da hurumin fadin darajar kudinsu, da yadda za su iya jingina kudin da euro ko dalar Amirka da sauran kudaden duniya."

Elfenbeinküste Abidjan | Alassane Ouattara, Präsident & Emmanuel Macron, Präsident Frankreich

Macon da Ouattara ne suka karkata akalar CFa zuwa ECO

Soke jingina kudi a baitilmalin Faransa 

Matakin soma amfani da kudin ya tanadi soke ajiye kudadan ajiya da babban bankin BCEAO na kasashen yammacin Afirka renon Faransa ma su kashe kudin CFA ke yi a babban bankin Faransa tun bayan samun mulkin kai, akwai kuma batun janyewar dukannin ‘yan Faransa daga jagorancin kungiyar UEMOA ta kasashen yammacin Afirka masu amfani da kudin na CFA da kuma bankin na BECEAO, wanda ake ganin tamkar wani ci gaba ne a kokarin da kasashen ke yi na samun dogaro da kai ta hanyar abun da ya shafi tattalin arzikinsu.

A yanzu dai kallo ya koma zuwa ga kasashen nan takwas na UEMOA masu amfani da kudin CFA a yammacin Afirka, ganin ko za su rungumi wannan tsari na kudadan ECO ko kuma za su jira har lamarin ya kasance a karkashin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO mai mambobi 15 cikinsu har da kasashen Najeriya da Ghana da ke zama na kan gaba ga a jerin kasashen ta fannin tattalin arziki.

Sauti da bidiyo akan labarin