Taron AU kan tsaro da Ebola a Afirka | Labarai | DW | 30.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron AU kan tsaro da Ebola a Afirka

Taron shugabannin kasashen Afirka na shekara-shekara na wannan karon zai maida hankali kan kalubalen tsaro a Najeriya da kuma cutar nan ta Ebola a Afirka.

Nkosazana Dlamini-Zuma

Shugabar kungiyar kasashen Afrika ta AU Nkosazana Dlamini-Zuma

Gabannin taron na yau dai, shugabar kungiyar ta AU Nkosazana Dlamini-Zuma ta yi kiran hada karfi a karfe wajen dakile aiyyukan masu kaifin kishin addini da ke cin karensu ba babbaka a wasu kasashen nahiyar.

Tuni dai kwamitin tsaro da zaman lafiya na AU din ya bukaci a samar da wata rundunar soji mai yawan dakaru dubu 7 da dari 5 domin kawo karshen tada kayar bayan 'yan bindiga.