Taron Afirka da EU zai duba batun samar da aiki da kwanciyar hankali a Afirka | Labarai | DW | 29.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron Afirka da EU zai duba batun samar da aiki da kwanciyar hankali a Afirka

Shugabannin Afirka da na kungiyar EU fiye da 80 sun hallara a birnin Abidjan don gudanar da taron hadin gwiwa don duba bukatun Afirka.

Fiye da shugabanni 80 na kasashen Afirka da Tarayyar Turai sun hallara a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire inda za su gudanar da wani taron hadin gwiwa da ke da nufin kirkiro guraben aikin yi da tabbatar da kwanciyar hankali a nahiyar Afirka mai samun bunkasar al'umma fiye da kima.

Wasu na kira da a kirkiro da sabon shirin Marshall Plan, shigen wanda aka yi amfani da shi aka tallafa wa Jamus bayan yakin duniya na biyu.

Taron na yini biyu da ake budewa a wannan Laraba ya zo ne yayin da kungiyar Tarayyar Turai EU ta farga cewa makomarta na da alaka da yawan bakin haure da ke gudu daga Afirka zuwa Turai da kuma batun hare-haren 'yan ta'adda.

Taron ya kuma zo ne a daidai lokacin da kasashen China da Indiya da Japan da kasashen yankin Gulf ke gogayyar samun angizo a nahiyar Afirka, inda har yanzu kungiyar EU ta kasance babbar mai taka rawa a fannin tattalin arziki da siyasa.