Tarayyar Turai za ta tallafawa Afirka da sama da Euro miliyan dubu uku da dari shida don dakile matsalar ′yan gudun hijira. | Labarai | DW | 11.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tarayyar Turai za ta tallafawa Afirka da sama da Euro miliyan dubu uku da dari shida don dakile matsalar 'yan gudun hijira.

Shugabanin kasashen kungiyar Tarayyar Turai na shirin tallafawa nahiyar Afirka da Euro Biliyan 3.6 a kokarin su na taimakawa wajen magance matsalar kwararar 'yan gudun hijira zuwa Turai.

Entwicklungstage in Brüssel

Taron dai zai karbi bakuncin sama da shugabanni 50 da suka fito daga tarayyar Turai da Afirka a wani yunkurin baya-bayan nan da Turai take na duba daukar matakan magance kwararar 'yan gudun hijirah daga Afirka zuwa Turai.

Kazalika tallafin kudaden daTarayyar Turan za ta bayar za a yi amfani ne dasu wajen daukar matakan karfafa harkokin tattalin arzikin masu son neman mafaka ne zuwa Turai.

A yayin da yake magana da manema labarai kwamishinan harkokin 'yan gudun hijirar na kungiyar EU Dimitris Avramopoulos yace kasashen Turan za su ci gaba da yau kaka danganta da kasashen Afirka don kare lafiyar 'yan gudun hijirar, gami da dakile safarar su zuwa Turai.