Tarayyar Turai na shirin gaggauta korar ′yan gudun hijira da ba a amince da bukatunsu ba | Labarai | DW | 08.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tarayyar Turai na shirin gaggauta korar 'yan gudun hijira da ba a amince da bukatunsu ba

EU za ta ninka yawan ma'aikata a hukumar tsaron kan iyakokinta wato Frontex, domin kula da cibiyoyin karbar 'yan gudun hijira na farko a Italiya da Girka.

Treffen der EU Innenminister in Luxemburg

Taron ministocin cikin gidan EU a Luxemburg

Kasashen Tarayyar Turai EU, na son kafin nan da shekarar 2020 za su kashe fiye da Euro miliyan 800 wajen gaggauta tasa keyar masu neman mafakar siyasa da aka yi watsi da bukatunsu na neman mafaka cikin kasashen kungiyar. Wannan dai na kunshe ne cikin sanarwar bayan taron da ministocin harkokin cikin gidan kungiyar suka gudanar a Luxemburg. Hakazalika kungiyar za ta ninka har sau 10 yawan ma'aikata a hukumar nan ta tsaron kan iyakokinta wato Frontex, domin kula da cibiyoyin karbar baki na farko a kasashen Italiya da Girka. Ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maizière ya yi maraba da wannan matakin. Ya ce nahiyar Turai za ta iya ba da mafaka ne ga masu fuskantar tsangwama, idan wadanda ba sa bukatar kariya ba su shigo nahiyar ba ko kuma a gaggauta komawa da su gida.