Tarayyar Turai da Birtaniya sun kasa cimma matsaya
July 20, 2017Talla
Bisa bayanan da babban mai tattaunawa na EU Michel Barnier ya yi, kungiyar tarayyar Turai da kasar Birtaniya suna nisa da cimma daidaito a zaman taron da suke yi game da ficewar Birtaniyar daga kungiyar ta EU da aka fi sani da Brexit. Barnier ya fada a birnin Brussels cewa akwai bambamcin ra'ayi babba kan 'yancin 'yan Birtaniya da 'yan kasashen EU da ke zaune a kasashen juna. To sai dai ministan Brexit na Birtaniya David Davis ya ce ya samu kwarin guiwa a tattaunawar. Bangarorin biyu dai sun bayyana haka ne bayan kammala zagayen farko na muhimman batutuwan da matakin ficewar Birtaniyar daga EU ya kunsa. A cikin watan Yuni bangarorin biyu suka fara tattaunawar.