1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Tanzania da Rwanda da Zimbabwe sun hana amfani da Benylin

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 16, 2024

Binciken masanan dai ya nuna cewa maganin yana kunshe da sinadarin Diethylene glycol mai hatsarin gaske, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar tarin kananan yara a kasashen Gambia da Kamaru da kuma Uzbekistan

https://p.dw.com/p/4eqz4
Hoto: mrp/imageBROKER/picture alliance

Kasashen Tanzania da Rwanda da kuma Zimbabwe, sun bi sahun wasu takwarorinsu na Afirka wajen janye maganin tari Benylin na kananan yara na kamfanin Johnson & Johnson daga kasuwanninsu, bayan wani binciken kimiyya a Najeriya ya gano maganin na da hatsari sosai ga lafiya.

karin bayani:WHO: Matakin kawar da magugunnan jabu

Sauran kasashen da suka dauki makamancin wannan matakin a baya, sun hada da Najeriya da Kenya da kuma Afirka ta Kudu. Ana dai amfani da maganin ne don tari da mura da zazzabi da kuma ciwon jiki ga kananan yara.

Karin bayani:Hanyoyin inganta lafiya a Afirka

Binciken masanan dai ya nuna cewa maganin yana kunshe da sinadarin Diethylene glycol mai hatsarin gaske, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar tarin kananan yara a kasashen Gambia da Kamaru da kuma Uzbekistan, daga shekarar 2022 zuwa yanzu.