Tallafin ƙasashen duniya ga Mali
May 16, 2013Talla
An yi ta ɗora alhakin rikicin Mali kan Abzinawan ƙasar, inda 'yan tawaye su ka yi amfani da damar hargitsin suka nemi aiyana yankin arewacin ƙasar a matsayin 'yantacciyar ƙasa. A watan Janairu bayan da Faransawa suka tura dakarunsu waɗanda suka haɗa gwiwa da dakarun Mali da na Afirka, sun yi nasarar fitar da 'yan tawayen daga arewacin ƙasar. Sai dai har yanzu akwai rahotannin hare-hare musamman a birnin Gao.
A yanzu haka dai, ƙasashe sun fara baiwa ƙasar tallafi domin ta sake gina kanta, ta kuma daidaita lamuran tsaro.
A ƙasa mun yi muka tanadin rahotanni daban daban kan halin da ake ciki a ƙasar ta Mali