1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gudummawar Jamus ga kokarin warware rikicin Mali

February 28, 2013

Majalisar dokokin Jamus ta amincewa gwamnatin kasar ta tura dakaru zuwa Mali domin bayar da horo ga sojojin kasar sabbin dabarun yaki.

https://p.dw.com/p/17oOR
Pioner von der malischen Armee Quelle: http://www.youtube.com/watch?v=TTunVQwPyHw&list=PL7466FFAAC01DBA55 Copyright: Bundeswehr
Hoto: Bundeswehr

Tun wasu watanni kenan kasar Mali ke daukar hankalin kasashen duniya, inda a farkon wannan shekara aka ga tamkar 'yan tawayen Islama daga arewacin kasar sun ci karfin rundunar sojin kasar kuma suna dab da kwace ragamar mulki. Kutsen da sojojin Faransa suka yi a tsakiyar watan Janeru ya katse musu hanzari. Tun daga lokacin aka fara girke sojojin kasashen Afirka a kasar, yayin da kasashen yamma ciki har da Jamus suka alkawarta ba da kayan aiki da jami'an da za su horas da sojojin Mali. Sai dai abin da ba a sani ba shi ne tun wasu shekaru da suka wuce Jamus ke a kasar ta Mali. Mohammad Nasiru Awal na dauke da karin bayani.

Sannu a hankali wata rundunar gamaiyar habaka tattalöin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ko CEDEAO za ta karbi ragamar aikin sojojin Faransa a Mali. A lokaci daya tarayyar Turai za ta karfafa aikin horas da sojojin Mali, kuma za ta dogara da kwarewar rundunar Jamus a kasar, domin tun kimanin shekaru bakwai da suka gabata sojojin Jamus ke kasar ta Mali, abin da da yawa daga cikin Jamusawa ba su sani ba. Tun daga shekarar 2005 har zuwa barkewar rikicin kasar a watan Afrilun shekarar 2012 wata tawagar masu ba da shawara ta rundunar Bundeswehr a Mali, inji wani jami'in soji a ma'aikatar tsaron Jamus a hira da tashar DW:

Ya ce: "Muna taimaka wa sojojin Mali, mun gina wata runduna wadda yanzu ta zama bangare na baradan sojojin ECOWAS. Bugu da kari mun kafa wata cibiyar horas da makanikai da sauarn kayan aikin soji."

Soldiers from the Tuareg rebel group MNLA ride in a pickup truck in the northeastern town of Kidal February 4, 2013. Pro-autonomy Tuareg MNLA fighters, whose revolt last year defeated Mali's army and seized the north before being hijacked by Islamist radicals, have said they are controlling Kidal and other northeast towns abandoned by the fleeing Islamist rebelsPicture taken 4, 2013. REUTERS/Cheick Diouara (MALI - Tags: CIVIL UNREST POLITICS CONFLICT) // eingestellt von se
'Yan tawayen MLNA a MaliHoto: Reuters

Tallafin Jamus ga Mali gabannin yaki

Jami'in soji wanda ya ce ka da a bayana sunansa, tun da farko ya ke jagorantar tawagar dake ta kunshi sojoji bakwai, kuma tun a farkon watan Farbrairu ya koma birnin Bamako don dorawa daga inda tawagar ta kwana a cikin watan Afrilun bara.

A lokacin da tawagar ta fara aiki a Mali a shekarar 2005, rundunar sojin kasar ba ta da kwarewa ta a zo gani, sannan tana da karancin kayan aiki, sai dai bisa taimakon Jamusawan a kasa da kuma kayan aiki, sannu a hankali rundunar ta Mali ta dan farfado. A karkashin shirin taimakon daga shekarar 2007 zuwa 2011, Jamus ta ba wa Mali kayan aikin soji fiye da na Euro miliyan uku. Kuma yanzu gwmnatin tarayyar Jamus za ta ci-gaba da wannan aiki karkashin shirin horaswa na kungiyar tarayyar Turai.

Yanzu da jami'in sojin na Jamus ya koma Mali, shi me ya fi daukar hankalinsa?

Ya ce. "Ni kan abin da ya burge ni kuma ke zama babbar nasara, shi ne bayan mun fice a bara sakamakon rikicin siyasa da kuma yaki a Mali, shi ne, cikin basira da kuma kwazo, sojojin kasar sun ci gaba da gudanar daya daga cikin aikace aikace mu wato cibiyar koyan sana'o'i."

HANDOUT - Das undatierte Handoutfoto zeigt Soldaten beim Entladen einer deutschen Transall der Bundeswehr in Bamako, der Hauptstadt von Mali. Drei deutsche Transportflugzeuge unterstützen den Einsatz der französischen Armee und ihrer afrikanischen Verbündeten gegen die Aufständischen in Mali. Foto: Bundeswehr/dpa (ACHTUNG: Nur zur redaktionellen Verwendung mit Urhebernennung «Foto: Bundeswehr». Das Bild darf nicht verändert werden.)
Dakarun Jamus a MaliHoto: picture-alliance/dpa

Sabbin dabarun yaki ga sojojin Mali

Yanzu dai Jamus za ta tura sojoji 40 karkashin lemar tarayyar Turai. Elke Hoff masaniyar harkokin tsaro ce ta jam'iyar FDP, ta ce aikin horaswan shi ne mafi alheri domin duk wani matakin soji ba zai iya maye gurbin matakin siyasa da ake bukata ba.

Ta ce: "Mun horas da kuratan sojoji kuma za mu ci-gaba da haka domin aikin wadannan sojoji yana da muhammanci a wata kasa kamar Mali. Abin da muka sa gaba shi ne tone abubuwa masu fashewa ko aikin gina hanyoyi da gadoji."

Sojojin na Jamus dai na ganin aikinsu a Mali zai dauki lokaci mai tsawo. Ita ma 'yar siyasar ta jam'iyar FDP Elke Hoff wadda a kwanan ta yi rangadin ganewa ido halin da ake ciki a kasashen Mali, Nijar da Aljeriya, ta yi fatan za a ci-gaba da tattaunawa da nufin warware rikicin na arewacin Mali.

Mawallafi : Mohammad Nasir Awal
Edita : Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani