1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta samu tallafi don sake gina kasar

May 15, 2013

Kasashen duniya da masu bada agaji na kasa da kasa sun yi alkawarin baiwa Mali tallafin kudi da yawansu ya kai kusan euro miliyan dubu uku da rabi domin sake ginar kasar.

https://p.dw.com/p/18Yic
Hoto: Reuters

Yayin taron dai, mahalartansa sun yi alkawarin tattarawa kasar ta Mali euro miliyan dubu uku da kusan rabi sabanin euro miliyan dubu biyu da a baya aka shirya tattarawa kasar inda kasar Faransa ta ce za ta bada gudumawar euro miliyan dari biyu da tamanin yayin da Jamus ta yi alkawarin bada tallafin euro miliyan dari wanda ta ce za ta biya a hankali daga yanzu zuwa badi, sai kuma Burtaniya da ce za ta agaza da euro miliyan dari da ashirin da takwas da nufin tabbatar da tsaro a Mali din da ma dai yankin Sahel baki daya.

Ita kuwa tarayyar Turai tun a jiya ta ce ta ware euro miliyan dari biyar da ashirin wanda za ta aikewa Mali din cikin shekaru biyun da ke tafe.

Da ya ke jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron na yau shugaban hukumar Tarayyar Herman Van Rompuy ya ce yunkurin da kasashen duniya su ka yi na gazawa Mali din 'yar manuniya ce ta shaukin da kasashen duniya ke da shi na ganin an sake gina kasar da ma dai ceto ta daga irin halin da ta tsinci kanta a ciki na rikici bayan da masu kaifin kishin addini a arewacin kasar su ka dau makamai.

Mali Geberkonferenz in Brüssel
Mahalarta taron tallafawa MaliHoto: Georges Gobet/AFP/Getty Images

Tuni dai mahukuntan kasar ta Mali su ka nuna jin dadinsu dangane da wannan tallafi da su ka samu to sai dai tarayyar Turai da masu bada agajin sun ce ya kyautu mahukuntan na Mali su tabbata sun maido da kasar kan tafarkin demokradiyyar batun da shugaban rikon kwaryar kasar Dioncunda Traore ya ce su ma tsada ranar gudanar da zabe.

Ya ce ''gwamnatin rikon kwaryar Mali ta tsaida karshen watan Yuli domin gudanar da zabukan shugaban kasa da nufin sauke nauyin da ke kansu.''

Krise im Norden von Mali
'Yan tawayen arewacin MaliHoto: Reuters

Baya ga batun ware lokacin yin zabe, shugaba Troare ya ce gwamnatinsa ba za ta yi katsalandan ba kan harkokin zaben don ganin an yi adalci.

Ya ce ''ba zan shiga takara ba haka ma abin ya ke ga mambobin gwamnati na. Mun yanke wannan shawarar ce domin mu na ganin bai kyautu a ce mun shiga takara ba kuma mun kasance alkalai. Mu na da muradin ganin an yi zaben da ke cike da adalci kuma wanda jama'a za su amince da shi.''

To yaiyn da burin Mali ya cika na samun tallafi, kalubalen da ke gabanta na da yawa wadanda su ka hada da samar da ababan more rayu da aiyyukan yi da samar da ilimi gami da wadata al'umma kasar da abinci domin kuwa hukumar abinci ta duniya ta bakin shugabar ta Ertharin Cousin na cewar kimanin mutane dubu dari shidda galibinsu yara kanana ke fama da karancin abinci.

Wata babbar matsala kuma ita ce ta ganin cewar al'amuran kasuwanci sun inganta a kasar batun da ministan kudin kasar Tiene Coulibaly ya ce durkushewarsa ta sanya kasar shiga wani mawuyacin hali.

Abin jira a gani shi ne yadda kasar ta Mali za ta alkinta wadannan kudaden da aka yi alkawarin bata da nufin ganin an maido kasar kan tafarki madaidaici da ma dai girka halstacciyar gwamnatin da za ta ja ragamar kasar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman