Masu hannu da shuni sun kuduri aniyar taimaka wa Mali ta fita daga halin kunci
May 14, 2013Wannan babban taro da zai hada wakilan kasashe masu hannu da shuni da kuma kungiyoyin bada agaji na kasa na kasa, na da burin tattara akalla tsabar kudi Euro miliyan dubu biyu, wanda za a amfani da su wajen sake gina yankin arewacin Mali da yaki ya kacencana, da kuma tabbatar da tsaro cikin kasar.
A ganawar da aka yi makon da ya gabata, tsakanin shugabar Gwamnatin Jamus da shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar, Merkel ta jaddada mahimmancin hada wannan kudade domin taimakawa Mali.Taron na birnin Brussels zai wakana a daidai lokacin da dakarun gwamnatin Mali suke darkakawa zuwa yankin Kidal, wanda ke cikin hannun kungiyar tawayen MNLA ta abzinawa.
A cewar Ulrich Delius shugaban dake kula da sashen Afrika a Kungiyar Kare hakkokin jama'ar dake cikin baraza wato GfbV wadda ke da cibiyarta a Jamus, ya baiyana zullumin sojojin su wuce gona da iri a kokarinsu na kwatar Kidal daga kungiyar MNLA.
"Mun zuba ido muga yadda sojojin Mali zu su kaddamar da gwagwarmayar kwatar Kidal, za su kiyaye hakkokin abzinawa wanda ba su dauki makamai ba,ko kuma za su gama jiji da jar kanwa.A gaskiya muna cikin zullumi."
A watan Maris na shekara 2012 kungiyar MNLA ta karbi yankin Kidal kamin daga bisani Kungiyoyin MUJAO da Ansar-Deen su kore su.
Sun sake mamaye Kidal bayan da sojojin Faransa suka fattafaki kungiyoyin masu kaifin kishin addinin Islama daga yankin.
Sojojin Mali sun kuduri aniyar sake kwatar Kidal, domin tabbatar da tsaro cikin kasar kamin zaben shugaban kasa na watan Juli nan wanan shekara.
To saidai a cewar Ulrich Delius abin da kamar wuya Mali ta yi nasara shirya zabe a cikin wannan wa'adi:
"Akwai matsalolin masu yawa tattare da wannan zabe.Misali a halin yanzu, akwai 'yan gudun hijira fiye da dubu dari hudu a kasashen makwafta da kuma wanda ke cikin kasar, cilas suma su yi zabe.
A yanzu babu wani tsari da tanada.Zai wahala a iya shirya zabe watan Juli na wannan shekara" .
Su ma dai kungiyoyin kasa da kasa sun baiyana bukatar ganin Mali ta shirya wannan zabe, domin mika mulki da zabbabiyar gwamnati, to amma a cewar Annette Lohman, shugabar Gidauniyar Friedrich Ebert Stiftung dake birnin Bamako akwai matsaloli biyu da ta kamata taron kasa da kasa na Beljiyam ya fi maida hankali akai:
"Al'umar dake yankin arewacin kasar na cikin kuncin rayuwa.Suna fama da karanci abinci, da karancin asibitoci sannan uwa uba matsalolin tsaro.Kamata tayi a bullo da wani tsari kwakkwara na raya wannan yanki."
A nasu gefe,Kungiyoyin kare hakkokin Bani Adama na kasa da kasa, sun bukaci kasashe da kungiyoyi masu hannu da shuni wanda za su taimakawa Mali,su yi la'akari da kare hakkokin Bani Adama, mussamman a daidai wannan lokaci da gwamnatin kasar ta baiyana aniyar kwatar Kidal ta ko wane hali.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman