Tallafin Asiya ya yi kaɗan a yaƙi da Ebola | Labarai | DW | 04.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tallafin Asiya ya yi kaɗan a yaƙi da Ebola

Da dama cikin ƙasashen a yankin Asiya na nuna halin ko in kula a ƙoƙarin da duniya ke yi na ganin an kawo ƙarshen cutar Ebola a yammacin Afirka.

Jim Yong Kim Präsident Welt Bank

Jim Yong Kim shugaban Bankin Duniya

Duk kuwa da ƙwarewar da wadannan ƙasashe ke da ita a fannin ma'aikatan kula da lafiya a cewar shugaban bankin duniya Jim Yong Kim a ranar Talatan nan ba sa abin da ya dace.Mista Kim ya faɗi a taron manema labarai a birnin Seoul cewar ƙasashe da dama a yankin na Asiya da za su iya ba da gudunmawa ba sa yi musamman idan ana maganar tura jami'an lafiya .

Dubban ma'aikatan lafiya a ke buƙata a yaki da wannan annoba, tun lokacin ta kafa tarihi a shekarar 1976, ya zuwa yanzu ta kashe sama da mutane 5000 a ƙasashen yammacin Afirka, mafi akasari a Guinea da Saliyo da Laberiya.