Taliban ta yi kisa a taron maulidi | Labarai | DW | 01.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taliban ta yi kisa a taron maulidi

Wasu mayakan Taöliban a Pakistan sun kashe mutane tare da jikkata wasu masu yawa a wata cibiyar horar da aikin gona a arewa maso yammacin kasar.

Rahotannin dake fitowa daga kasar Pakistan, na cewa wasu mayakan Taliban sun kashe mutane tara yayin kuma da wasu da dama suka jikkata. Lamarin dai ya faru ne a wata makarantar dake arewa maso yammacin Peshawar, lokacin da matasa ke bikin maulidi.

A cewar jami'an 'yan sandan kasar, 'yan bindiga uku ne suka buda wuta kan masu gadin makarantar da horar da harkokin noman, kafin su kutsa cikin dandazon jama'ar. Hukumomin sun kuma yi ikirarin kashe 'yan bindigar wadanda dukkaninsu ke dauke da jigidar bama-bama, tare da kakkabe wajen da lamarin ya faru. Dalibai shida ne dai aka tabbatar da mutuwarsu a harin na wannan Juma'a.