Taliban ta shirya kafa sabuwar gwamnati | Labarai | DW | 02.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taliban ta shirya kafa sabuwar gwamnati

Jagororin kungiyar Taliban a Afghanistan sun ce nan da dan lokaci kadan ne za su sanar da wadanda za su jagoranci sabuwar gwamnatin da za su kafa a kasar.

Kungiyar Taliban ta ce tana gab da kafa gwamnati a Afghanistan, a daidai lokacin da wasu matan kasar ke zanga-zangar neman yadda sabuwar gwamnatin za ta iya ba su 'yancin yin aiki.

Taliban din dai ta yi alkawarin samar da gwamnati mai sassaucin ra'ayi, sabanin jagorancin da ta yi a tsakanin shekarar 1996 zuwa 2001.

Ana kuma kallon jan aikin da ke a gaban kungiyar, na samar da sauyi a fannin gudanar da al'amura daga matsayin su na mayaka zuwa ga gwamnatin da duniya za ta yi na'am da ita.

A ranar Juma'ar da ke tafe ne dai ake sa ran jagororin na Taliban, za su sanar da sabuwar majalisar ministoci kwanaki kalilan da ficewar Amirka daga kasar.