Takaddama dangane da zaben gwamnoni | Siyasa | DW | 13.04.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaddama dangane da zaben gwamnoni

Tawagar Kungiyar Tarayyar Turai, da ta sa ido a zaben Najeriya ta nuna damuwa a kan karuwar tashe-tashen hankula a zaben gwamnoni, da karancin matan da suka sami nasara.

A rahoton da tawagar Kungiyar Taryyar Turan da ta sa ido a zaben na Najeriya ta gabatar dazu nan a Abuja ta nuna damuwa a kan sake fuskantar matsaloli a zaben na Najeriya, musamman a wuraren da ta ce sam ba'a ma yi aiki da na'urarar tantanace yatsar hannu ba, tare ma da gaza samun izinin yin zabe musamman ga mutane milyan 2.3 a zaben shugaban kasa duk da cewa an tanatance su.

Shugaban tawagar Kungiyar Tarayyar Turan da suka sa ido a zaben na Najeriya a jihohin 18 Santiago Fisas ya bayyana cewa abin damuwa irin yadda aka fuskanci matsaloli na sace akwatinan zabe dama tashe-tashen hankula wanda ya ce ba abinda za'a lamunta bane.

‘Abin takaici ne yadda mutane da yawa suka rasa rayyukansu a ranar jefa kuri'a dole ne fa zabe ya kasance an yi shi cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali , ya kamata ‘yan kasa su samu damar bayyana zabinsu na siyasa a cikin kwanciyar hankalai ba tare da tsoron rayuwarsu ba. Matsalolin sun fi tsanata a jihohin Rivers da Akwa Ibom inda aka samu rahotanin tashe tashen hanklua, wannan na nuna bukatar gudanar da bincike'.

Tawagar ta sanya ido har a kan kafafen yada labarai

Nigeria Wahlbeobachter

Tawagar EU ta nuna damuwa

Tawagar ta Kungiyar Tarayyar Turan dai da ta baza jami'anta har 315 da suka sanya idannu a zaben na Najeriya inda a karon farko ta sa ido a kan kafofin yada labaru na gwamnati da masu zaman kansu da suka hada da gidajen radiyo 8 da na Telbishin guda 3 da jaridu 3. Hannah Roberts it ace matakaimakiyar shugaban tawagar da suka yi nazarin ta bayyana abinda suka gano

‘Mun gano cewar biyo bayan samaun nasarar lashe zaben shugaban kasa da jam'iyyar APC ta yi, ana samun karuwar dauko rahotani a kan al'amuran jamiyyar, abinda ya samar da dai daito da jamiyya mai mulki, to sai dai bata canza zani ba a matakin jihohin inda jamiyyar da ke mulki ke mamaye lamarin, abinda ya sabawa dokar samar da daidaito ga dukkanin yan takara'.

Tawagar za ta ci gaba da kasancewa a Najeriya har zuwa watan mayu kafin ta fitar da kamalallen rahotonta tare da ba da shawarwari a wuraren da take ganin akwai bukatar gyara.

Sauti da bidiyo akan labarin