Taimakon yara marayu ′yan gudun hijira | Himma dai Matasa | DW | 29.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Taimakon yara marayu 'yan gudun hijira

Kungiyar daliban makarantun kimiyya da fasaha ta Tarayyar Najeriya na tallafawa yaran da suka rasa iyayensu a rikicin Boko Haram, ta hanyar basu kulawa a fannin ilimi.

Daruruwan yara ke fuskantar rashin ilimi sakamakon Boko Haram

Daruruwan yara ke fuskantar rashin ilimi sakamakon Boko Haram

A wani matakin rage yawan kananan yara ‘yan gudun hijira da kungiyar Boko Haram ta hallaka iyayensu, a karan farko wata kungiyar dalibai ta bullo da wani tsarin ilmantar da kananan yara marayu ‘yan gudun hijira, ta hanyar daukar dawainiyar karatunsu kama tun daga firamare zuwa sakandare domin yakar jahilci. Kungiyar daliban manyan makarantun Najeriya ce dai ta bullo da wani sabon salon ilmantar da kananan yara ‘yan gudun hijira marasa iyaye daga sansanin ‘yan gudun hijiran wadanda aka kwaso daga Arewa maso Gabashin kasar da ke zama tare da daliban a cikin makarantunsu, domin horar da su ta hanyar wani tsarin karatun da suka kirkiro mai taken ”Up-Camp education system” da zummar magance karancin ilmi da ke addabar miliyoyin kananan yara marayu ‘yan gudun hijirar. Mr Adikpee odeh shi ne shugaban daliban kwalejin kimiyya ta jihar Kaduna, ya kuma ce dole ne su tashi tsaye domin tabbatar da ganin cewa sun bayar da tasu gudunmawar a kan ceto dubban kananan yara marayu 'yan gudun hijira da ke matukar fama da matsalar rashin zuwa makaranta.

Baya ga haka ma dai, akwai wani tsarin karantarwa da daliban suka bullo da shi na daukar dawainiyar maraya kama tun daga ilminsa da ciyarwa tare da tufatar da shi da kuma horar da su wasu kananan sana'ao'in hannu don su zamo masu dogaro da kansu a nan gaba. Bugu da kari kungiyar daliban yanzu haka na tattara littatafai daga hannun ‘yan Najeriya tare da rarrabawa sauran kananan yara ‘yan gudun hijira mazauna sansanoni daban-daban da ke yankin na Arewa maso Gabashin Najeriyar, domin tabbatar da gain kowanne dan kasar ya bada tasa gudun mawar akan ilmin marayu.

Sauti da bidiyo akan labarin