Taimakon masu cutar yoyon fitsari a Nijar | Himma dai Matasa | DW | 29.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Himma dai Matasa

Taimakon masu cutar yoyon fitsari a Nijar

A Jamhuriyar Nijar wasu rukunin kungiyoyin mata ne suka samar da wata cibiya, da ke bai wa mata masu matsalar yoyon fitsari mafaka a yayin da suke fuskantar kyama daga danginsu.

Mata na fuskantar kalubalen rayuwa a Afirka

Mata na fuskantar kalubalen rayuwa a Afirka

Cibiyar na horar da matan ayyukan hannu don samun wata sabuwar rayuwa da kuma daukar dawainiyar kula da lafiyarsu. Duk da yake kawo yanzu ba'a kai ga tabbatar da ko mace nawa ke dauke da cutar ta yoyon fitsari a Jamhuriyar Nijar ba, to amma an san adadin alkalumman abin da ke haifar da matsalar wanda masana ke misaltawa galibi da rashin isassun asibitoci da rashin binciken lafiyar masu juna biyu da ma wasu lokutan auren wuri da tsabagen talauci da fatara, wadanda ke taka mahimiyar rawa wajen hana dakile wasu abubuwan da ke kan gaba wajen habaka cutar ta yoyon fitsari, wadda kuma ke janyo kyama da rashin kauna da tsangwama ga duk wacce ta kama. Aisha Habubakar yarinya ce yar kimanin shekaru 20 da ke rataye da 'yar jikarta da ke tallafa mata rike futsarin, ta kuma ce ta kamu da cutar ne sakamakon haihuwa sanadiyyar rashin samun kulawar da ta kamata a yayin da take da juna biyu da ma yayin da take nakuda.

Cibiyar mai suna Dimol, wato diyauci a hausance inda Aisha da wasu tarin mata ke samun mafaka bayan fuskantar matsalar tsangwama sakamakon cutar da ke addabarsu, wasu kungiyoyin mata ne suka kirkiro tare da kafa cibiyar. A kalla macce bkwai ke shiga wannan cibiyar ko wane wata. Mme Fanta Ba ita ce daraktar cibiyar, ta ce a tsahon zaman da matan zasu yi a cibiyar suna koyon aikin hannu domin idan sun warke sai a kai su gida a kuma basu jarin da za su yi sana'a.

Sauti da bidiyo akan labarin