Taimakawa mabukatu na musamman | Zamantakewa | DW | 29.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taimakawa mabukatu na musamman

Hukumominin Nijar sun dauki matakai na kafa kwamitoci domin aiwatar da shirin al'amuran da suka shafi gajiyayyu da ke fadin kasar baki daya

Dama dai tun can farko a lokacin rikon kwarya na gwamnatin Salu Jobo ne aka kafa babban komiti na kasa ba tare da an yi masa rassa a cikin kasar ba. To ko me ke dalilin tsara wannan tafiyar a yanzu?

Allassan Issa shugaban ma'aikatar dake kula da al'umma wace ta shirya taron cewa yayi:

Wannan sabon tsarin ne zai basu damar cin moriyar tallafin da gwamnati da ma wasu kungiyoyin agaji suka musu tanadi inji malam Salifu Suleiman shugaban hadin gwaiwar kungiyar gajiyayyun.

Kazalika, suma marasa gani da ido na da irin nasu matsalolin inji malam Garba Haruna shugaban kungiyar marasa gani da ido.

Ko wacce daga cikin ma'aikatar da aka sa cikin wannan komitin zata kawo iya nata gudunmawa. Malam Habibu Ibrahim, dake zaman shugaban ma'aiktar dake kula da ayyukan hannu ya ce, su kam suna sauke nauhin da aka rataya musu zuwa ga gajiyayyun.

Wannan dai shi ne karo na farko da aka taba shirya irin wannan tsarin a Janhuriyar Nijar.