Taba Ka Lashe(15.05.2019) | Zamantakewa | DW | 21.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taba Ka Lashe(15.05.2019)

Shirin ya duba tarihin rayuwar Sharif Rabi'u Usman Baba shahararren mawakin begen Manzon Allah wanda Allah ya yi wa rassuwa a wannan wata na Mayu a birnin Kano na Tarayyar Najeriya.

Saurari sauti 09:56

Shirin Taba ka Lashe na wannan karo ya duba tarihin rayuwar marigayi Rabi'u Usman Baba fitaccen mawakin begen Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi na birnin Kano a Tarayyar Najeriya, tasirin da ya yi kan sha'irai a zamaninsa da kuma gudunmawar da ya bayar wajen cusa soyayyar manzon Allah da ahil baiti gidansa da ma waliyyan Allah a cikin zukatan Musulmi a duniya.