1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karamar kabilar Igdaalan na neman ta shiga harsunan Nijar.

Mohammad Nasiru Awal AAI
October 22, 2019

Karamar kabilar Igdaalan na neman shiga harsunan Nijar.

https://p.dw.com/p/3Rjzx

A jamhuriyar Nijar, a kwanakin baya ne a birnin Yamai aka gudanar da wani taro da ya hada masana tarihin zamantakewar al'umma da sarakunan gargajiya, domin yin nazari kan harshen wata karamar kabilar kasar da ake kira Igdaalan, da ke fatan hukumomi su saka ta cikin jerin harsunan jamhuriyar ta Nijar. Kabilar tana nan ne a yankin Hamada kuma tana da alaka da Abzinawa da Larabawa. Ana samun wannan al'umma a cikin jihohin Agadez Maradi da kuma Tahoua. 

Kabilar ta Igdaalan daya ce, daga cikin kananan kabilun wannan kasa da ke da dangantaka da kabilun kasa da yawa ciki har da Abzinawa. Sai dai kasancewa harshenta ba shi daga cikin jerin harsunan kasar a hukumance, shugabanninta suka yi wannan babban taro da zumar ganin an sanya harshenta a jerin harsunan kasar ta Nijar kamar yadda Intinikar Alasan na jam'iyyar PNPD dan Igdaalan ya yi karin haske.