Sumame kan ′yan Boko Haram a Abuja | Labarai | DW | 20.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sumame kan 'yan Boko Haram a Abuja

Wani sumame da jami'an tsaron Najeriya suka kai a Abuja ya yi sanadiyyar rasuwar wasu mutane da jami'an tsaron suka ce 'yan kungiyar nan ce ta Boko Haram.

Sojoji da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya ta tarayyar Najeriya sun kai wani samame inda suka kashe mutane tara da suka ce 'yan Boko Haram ne a kusa da unguwar ‘yan majalisun tarayyar kasar da ke Apo a Abuja.

Jami'an tsaron dai sun ce sun kai sumamen ne da taimakon da suka samu na bayanan sirri da wani mutum da ake zargin dan kungiyar ne ya basu.

Merlyn Ogar ita ce kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya wato SSS, ta kuma yi wa manema labarai karin haske ciki kuwa har da wakilinmu na Abuja Uwais Abubakar Idris, inda ta ce hadin gwiwar sojoji da jami'an hukumarsu ne suka kai harin har ma suka samu nasarar kashe tara da kuma kama wasu sha biyu wanda yanzu haka suke wa tambayoyi.

To sai dai yayin da jami'an tsaro ke cewar mutanen da aka kashe da wanda aka kama 'yan Boko Haram ne, wani da ya samu tsira da ransa daga harbe-harben ya ce wasu mutane da ke kananan sanao'i ne ke kwana a gidan da aka kai harin.