1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan kwallon kafar La liga sun kamu da coronavirus

May 10, 2020

Wasu 'yan wasa guda biyar na kasar Spain da ke buga wasannin kwallon kafa a gasar La liga sun kamu da coronavirus. Mahukumtan La liga din ne suka tabbatar da haka a wannan Lahadi. 

https://p.dw.com/p/3c0TV
Spanien Fußball Logo erste Liga La Liga Logo
Hoto: picture-alliance/AA/B. Akbulut

A makon da ya gabata ne dai aka fara amincewa wasu 'yan wasa a Spain din su fara atisaye a kokarin da mahukumta ke yi na sake bude gasar kwallon kafar a watan Yuni mai zuwa. Sai dai kafin kai wa ga wannan mataki hukumomi sun ce sai sun yi wa 'yan wasan gwajin corona, wanda a haka din ne kuma aka gano wadannan 'yan wasa guda biyar da ba a bayyana sunansu a hukumance ba.

Sai dai mahukumtan La ligar sun ce an kebe 'yan wasan kuma za a ba su kulawar likita, sannan za a amince su dawo fagen wasa ne kawai idan har an gwada su sau biyu ba a same su da cutar ba.