Soma aikin rundunar yaki da safarar bakin haure | Labarai | DW | 19.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Soma aikin rundunar yaki da safarar bakin haure

Kasashen sun ce shawo kan sabanin da ke da akwai a tsakaninsu sannan sun tanadi kayan aiki da su ka hada da jiragen sama da na ruwa.

A ranar litanin mai zuwa ne ministocin harakokin kasashen wajen Tarayyar Turai za su kaddamar da rundunar tsaron tekun baharum wacce za ta kalubalanci kungiyoyin masu safarar bakin haure ta teku zuwa Turai.Kasashen Tarayyar Turan sun ce kawo yanzu sun kammala duk tsare tsaren da aikin ya ke bukata kuma sun shawo kan duk wani sabani da ke da akwai a tsakaninsu kan wannan batu.Tuni kuma suka tattara jiragen ruwa da na sama wadanda za a wannan aiki da su.Ainahi dai aikin wannan runduna shi ne kai hari a kan jiragen da ke safarar bakin hauren.

To amma kafin kwamitin sulhu na Majalissar Dinkin Duniya ya ba da na'am dinsa, aikin rundunar zai tsaya ga tsaron iyakokin ruwa da musanyan bayanai a kan kungiyoyin masu safarar bakin haren