1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sokoto: Fasinjoji sun kone a harin 'yan bindga

December 8, 2021

Rahotanni daga jihar Sokoton Najeriya na nuni da cewa kimanin fasinjoji 30 na wata motar bas ne suka kone kurmus ciki har da mata da kuma yara bayan da 'yan bindiga suka cunna wa motarsu wuta.

https://p.dw.com/p/43zg3
Nigeria Region Borno Boko Haram
Hoto: Audu Ali Marte/AFP/Getty Images

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigar sun kai wa fasinjojin harin kwanton baunar ne yayin da suke tafiya a hanyar da ta hada karamar hukumar Sabon Birni da kuma kauyen Gidan Bawa a jihar Sokoto. Wasu mazauna kauyen da suka kai dauki wurin da hatsarin ya auku sun bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa, motar cike take makil da fasinjoji kuma ba a iya tantance gawawwakin.

Kakakin rundunar 'yan sanda a yankin arewa maso yammacin jihar Sokoton Sunusi Abubakar ya ce tuni aka mika wadanda suka jikkata zuwa asibiti. A shekarun baya-bayan nan dai 'yan bindiga a arewacin Najeriya sun zafafa kai hare-hare musamman a yankunan karkara da kuma yin garkuwa da mutane da kuma dalibai don neman kudin fansa.