Sojojin Siriya sun kaddamar da gagarumin farmaki a lardin Homs | Labarai | DW | 15.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Siriya sun kaddamar da gagarumin farmaki a lardin Homs

Hare-haren da sojojin na Siriya ke kaiwa tare da tallafin Rasha sun halaka mutane da dama ciki har da 'yan tawaye a yankin na Homs.

Sojojin Siriya da ke samun taimakon jiragen saman yakin kasar Rasha sun kaddamar da gagarumin farmaki a lardin Homs da ke tsakiyar kasar. Tashar telebijin din kasar ta rawaito majiyoyin soji na cewa an fara kai harin ne a arewaci da kuma arewa maso yammacin lardin. Kungiyar 'yan adawa mai sanya ido kan batun kare hakkin dan Adam a Siriya ta ce jiragen yakin Rasha sun kai hare-hare akalla 15 a yankin, inda suka kashe akalla mutane 10 ciki da 'yan tawaye shida. Kungiyar ta kuwa rawaito gwabza kazamin fada tsakanin sojoji da 'yan tawaye a kudancin yankin Talbisseh da ke hannun 'yan tawaye. Yankin dai na tsakanin biranen Homs da Hama.