Sojojin Saudiyya na barin wuta a Sana′a | Labarai | DW | 20.07.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Saudiyya na barin wuta a Sana'a

Mazauna kusa da Sana'a babban birnin kasar Yemen sun ce bakin hayaki ya tirnike sararin samaniya bayan da jiragen yaki suka kaddamar da bude wuta kan sansanonin 'yan tawayen Houthi.

Rahotanni da ke fitowa daga Sana'a babban birnin kasar Yemen na cewa sojojin yaki da Saudiyya ke jagoranta, sun fara kaddamar da hare-haren bama-bamai ta sama kan wasu muhimman cibiyoyin da 'yan tawayen Houthi ke iko da su a birnin.

Cikin wuraren da dakarun kawancen ke kai wa hari a sabon samamen sun hada da manyan cibiyoyin tsaron 'yan tawayen da rumbun adana makaman kare dangi da rokokinsu da ke birnin Sana'a.