1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tabbatar da mutuwar sojojin Nijar a kauyen Bobargu

Ramatu Garba Baba
November 7, 2018

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar wasu sojojin kasar biyu a yayin da wasu biyar suka sami rauni bayan da motarsu ta taka wata nakiya a kauyen Bobargu na Jahar Torodi

https://p.dw.com/p/37pqJ
Mali - Französische und malische Truppen töten in Mali 30 Dschihadisten
Hoto: Getty Images/AFP/P. Guyot

Lamarin ya auku ne a kauyen mai tazarar nisan kilo mita dari da goma daga Kudu maso Yammacin kasar. Duk da ya ke hukumomin kawo yanzu ba su fito sun bayyana kungiyar da ake zargi da kai harin ba, amma a 'yan kwanakin baya bayan nan mayakan jihadi na matsa kaimi tare da kai hare haren ta'addanci a yankin. A farkon makon jiya ne, gwamnatin kasar ta tura karin sojojinta a yankin don kakkabe mayakan jihadin da tace sun yi sansani a Kudu maso Yammacin kasar mai iyaka da kasar Burkina Faso.