Sojojin Nijar da na Amirka sun mutu a cikin Nijar | Labarai | DW | 05.10.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Nijar da na Amirka sun mutu a cikin Nijar

Wani harin kwantAn bauna ya hallaka sojojin Nijar da dama gami da na Amirka bayan da wasu mutane dauke da manyan makammai suka buda musu wuta a yankin jihar Tillabery da ke iyaka da Mali.

Mali Soldaten (picture-alliance/CITYPRESS24)

Sojan Nijar da na kasashen waje yayin da suke sintiri a iyaka da Mali

Wata majiya ta tsaro ta kasar ta Nijar ta shaida wa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP cewa, sun yi rashin sojoji da dama a yankin jihar Tillabery mai makwabtaka da kasar Mali ba tare da bada wani adadi ba. Sai dai rundunar sojojin Amirka a Afirka ta Africom ta tabbatar da mutuwar sojojin Amirka guda uku, wasu kuma sun jikkata, yayin da ita ma jaridar New York Times ta kasar Amirka ta tabbatar da mutuwar sojojin na Amirka uku yayin da kuma wasu guda biyu da suka samu raunuka.

Mai magana da yawun fadar shugaban Amirka Sarah Sanders ta sanar wa manema labarai a birnin Washington cewa Shugaba Donald Trump ya sami labarin harin na Nijar ba tare da ta yi wani karin bayani ba.

A tsakiyar watan Satumba ne gwamnatin Nijar ta tsawaita dokar ta baci a yankin jihar Tillabery da ke yammacin kasar da kuma Diffa da ke gabashi. Sai dai ya zuwa yanzu babu wani bayani daga hukumomin na Jamhuriyar Nijar.