Sojojin Najeriya sun jikkata Shekau | Labarai | DW | 23.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Najeriya sun jikkata Shekau

Rundunar Sojoji sun bayyana sunayen Abubakar Mubi da Malam Nuhu da Malam Hamman cikin manyan kwamandojin Kungiyar da aka hallaka a wannan hari.

Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa hari da mayakan ta na sama suka kai a sansanin Boko Haram ya hallaka wasu jiga-jigan kungiyar, inda suka yi nasarar naskasa Abubakar Shekau da ke cikin masu ikirarin shugabantar kungiyar.

Sanarwa da kakakin rundunar Sojojin Kanar Sani Usman Kuka Sheka ya fitar a ranar Litinin, na cewa sun kaddamar da hare-hare ne a ranar Juma'ar da ta gabata a kauyen Taye dake yankin Gombale, inda aka jikkata wasu manyan kwamandojin kungiyar.

Sanarwar ta kuma bayyana sunayen Abubakar Mubi, da Malam Nuhu da Malam Hamman a cikin sanarwar, wan da ke nuna cewa mutanen na cikin manyan kwamandojin Kungiyar da aka hallaka a hari. Amma kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da ikirarin Sojojin, kazalika su ma kungiyar ba su ce komai kan sanarwar sojojin ba.

A baya dai Sojojin sun sha ikirarin cewa sun hallaka shugaba Kungiyar Abubakar Shekau sai dai Kungiyar kan musanta ta hanyar wallafa faifen bidiyo da shugaban ke raddi.