Sojojin gwamnatin Siriya sun kashe fararen hula a Aleppo | Labarai | DW | 21.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin gwamnatin Siriya sun kashe fararen hula a Aleppo

Barin wutar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 18 a birnin da ke zama tungar 'yan adawa da shugaba Assad da ke arewacin Siriya.

Ruwan bama-bamai da dakaru masu biyayya ga shugaba Bashar al-Assad suka yi ya hallaka akalla fararen hula 18 a wata unguwa da ke birnin Aleppo na arewacin kasar. Shugaban kungiyar sa ido kan hakkin dan Adam a Siriya Rami Abdel Rahman ya fada wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa dakarun gwamnati sun yi barin wutar ne a kan unguwar Al-Shaar da ke gabashin birnin Aleppo, da ya kasance karkashin ikon 'yan adawa. Jami'in ya kara da cewa mutane da dama sun jikkata sannan har yanzu akwai wasu karkashin rusassun gine-gine.

A wani labarin kuma ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta yi kira da a dauki kwakkwaran mataki bayan da wani makami mai linzami ya afka wa harabar ginin ofishin jakadancinta da ke birnin Damascus, inda ta zargi dakarun da ke yakar shugaban Siriya Bashar al-Assad da aikatawa.