1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun kori 'yan Boko Haram a Borno

Al-Amin Muhammad/ MABMay 30, 2015

'Yan bindiga sun kwana suna harbe-harbe rokoki a Maiduguri. Sai dai kuma dakarun Najeriya sun yi nasarar fatattakarsu daga babban birnin na Borno.

https://p.dw.com/p/1FZTB
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Ikechukwu

Rundunar Sojojin Najeriya ta yi ikirarin murkushe wani hari da wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan Kungiyar Boko Haram ne suka kai a Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno. Bayanai sun nunar da cewar ‘yan bindigar sun harba rokoki cikin daren jiya Jumma'a zuwa Asabar a cikin garin na maiduguri, inda al’umma suka ce sun kwana su na jin karar harbe-harbe da fashewar abubuwa.

Bayanai sun nunar da cewa ‘yan bindigar wanda aka kiyasta cewar sun haurar ma 100 sun yi kokarin shiga babban birnin jihar Bornon inda su ka fara harba wadannan rokoki daga kauyen Dala dake bayan garin Maiduguri kafin jami’an tsaro su dakile kokarinsu.

Wannan hari wanda shi ne na farko tun bayan rantsar da sabon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jefa tsoro da firgita tsakanin al’ummar birnin Maiduguri wanda suka fara tunanin rabvuwa da hare-haren kungiyar.

Babu dai cikakken bayani na wadanda rokoki suka hallaka ko kuma nakasa a Maidiguri ya zuwa yanzu.