Sojoji 3 na NATO sun rasa rayuka a Afghanistan. | Labarai | DW | 20.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojoji 3 na NATO sun rasa rayuka a Afghanistan.

A ƙalla mutane 8 su ka rasa rayuka, a wasu sabin hare-hare da yan taliban su ka kai a yakuna kudu da gabacin ƙasar Afghanistan.

Wanda su ka mutum sun haɗa da sojoji 3 na ƙungiyar tsaro ta NATO yan ƙasar kanada.

Tun daga farkon wannan shekara, wannan su ne cikwan sojoji 91, na rundunar ƙasa da ƙasa da su ka mutu a Afghanistan.

Kakakin ƙungiyar yan taliban, Yusuf Hamadi ya sanar manema labarai cewar, hare-haren da su ka kai yau sunbiya da shugaban rundunar yan sanda na yankin Helmand, da su ke nema ruwa jallo.

Rundunar NATO, tare da haɗin gwiwar sojojin Afghanistan, sun ƙaddamar da wani gagaramin shiri, domin tunkara mayaƙan taliban, da su ka damƙe yakin Kandhar.