Sojin Ukraine sun karbe iko da Luhansk | Labarai | DW | 17.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Ukraine sun karbe iko da Luhansk

Rahotanni daga kasar Ukraine na cewar sojin kasar sun samu nasarar karbe iko da garin na Luhansk da ke ya jima a hannun 'yan aware.

Rundunar sojin Ukraine din da ta tabbatar da wannan labarin ta ce wannan nasara ta samu ne bayan da sojinsu suka shafe akasarin daren jiya suna fada da 'yan tawaye kuma yanzu haka sojin gwamnati ne ke iko da garin don tuni ma sun sanya tutar Ukraine din a guda daga cikin chaji ofis din da ke birnin.

A wani labarin kuma, 'yan waren da ke goyon bayan Rasha a Ukraine din sun harbo wani jirgin sojin a gabashin kasar inda ake tafka fada sai dai wata majiya ta soji ta ce matukin jirgin ya samu ya fita da ransa kuma har an dauke shi don duba lafiyarsa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu