Sojin Siriya sun soma yakin kwato yankunan kasar | Labarai | DW | 08.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Siriya sun soma yakin kwato yankunan kasar

Sojojin Siriyar masu samun dafawar jiragen sama da na ruwa na yakin kasar rasha sun kaddamar a wannan Laraba da hari ta kasa a wani yinkurin na sake kwato yankunan kasar daga hannun IS dama 'yan tawaye

Sojojin Siriya sun kaddamar a jiya Laraba da wani gagarimin hari ta kasa a wani yinkuri na neman kwato yankuna kasar da ke a hannun kungiyar 'yan tawaye dama Kungiyar IS. Sojojin gwamnatin ta Bashar al-Assad wadanda ke samun dafawar jiragen sama dama na ruwa na yaki na kasar Rasha na da burin a halin yanzu kwato babbar hanyar da hada birnin Damas da na Alep na arewacin kasar.

Shugaban Rasha Vladmir Poutine ya bada sanarwar cewa za su ci gaba da kai hare-haren da suka soma kaddamarwa a kasar ta Siriya inda a cewar ministan tsaron kasar ta Rasha Serguei Choigou a cikin mako daya, jiragen yakinsu sun kai hari a kan gurare 112 na mayakan Kungiyar ta IS a kasar ta Siriya.

Sai dai a jiya Laraba Amirka ta zargi kasar ta Rasha da fakewa da wannan dama domin kaddamar da wadannan hare-hare nata a kan mayakan 'yan tawayen kasar ta Siriya masu saussaucin ra'ayi da ke da burin kifar da gwamnatin Al-Assad.