Sojin Chadi sun kashe ′yan Boko Haram 207 | Labarai | DW | 25.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojin Chadi sun kashe 'yan Boko Haram 207

Dakarun Chadin sun sanar da hakan ne a ci gaba da gwabza fada da masu tsattsauran ra'ayin da ke kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Mayakan kasar ta Chadi sun sanar da cewa sun hallaka 'yan Boko Haram din a kusa da garin Garambu a yayin fafatawar da suka yi inda guda daga cikin sojojin kasar ta Chadi shima ya rasa ranasa. Kasashen Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar da suka fi makwabtaka da Tarayyar ta Najeriya sun dukufa wajen taimaka mata domin ta fatattiki 'yan Boko Haram din da suke gwagwarmaya da makamai a kasar. Ko da a wannan Talatar ma sai da mutane da dama suka rasa rayukansu sakamakon wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a tashoshin mota da ke garuruwan Kano da Potiskum. Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren sai dai ana dora alhakinsa a kan 'yan Boko Haram din.