Soji na ci gaba da sintiri a jihar Fatakwal a Nigeria | Labarai | DW | 18.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Soji na ci gaba da sintiri a jihar Fatakwal a Nigeria

Dakarun sojin Nigeria na ci gaba da sintiri a birnin Fatakwal din jihar rivers. Hakan ya biyo umarni ne da shugaba Yar´adua ya bayar ne, bayan wani mummunan tashin hankali da birnin ya fuskanta.Gwamnatin tarayyar dai tace daukar wannan mataki ya zama dole, don kare afkuwar abin da ya faru ga birnin.Arangamar data wanzu tsakanin tsageru na yankin da jami´an tsaro tayi sanadiyyar rayuka da daman gaske, banda wasu da dama da suka jikata.A ranar juma´ar data gabata ne gwamnatin jihar ta saka dokar ta baci, a kokarin inganta harkokin tsaro da zaman lafiya a birnin.Ya zuwa yanzu dai zaman lafiya ya fara inganta, kuma komai ya fara dawowa yadda yake kamar da.