1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine: Sojan Rasha ya nemi afuwa

Abdul-raheem Hassan
May 19, 2022

Wani sojan Rasha da ke fuskantar laifukan yaki a shari'ar farko tun fara yakin Ukraine, ya nemi gafarar wata mata da ya kashe bayan ya shaidawa kotu cewa ya yi hakane bisa umarnin shugabanninsa.

https://p.dw.com/p/4BaKX
Ukraine I Prozess gegen Vadim Shishimarin
Hoto: Jamie Wiseman/Daily Mail/dmg media/picture alliance

Sojan mai suna Sajen Vadim Shishimarin mai shekaru 23 a duniya, na fuskantar hukuncin daurin rai da rai idan kotu ta same shi da laifukan da ake tuhumarsa na bindige fararen hula a Ukraine a ranar 28 ga watan Febrairun wannan shekara da muke ciki ta 2022.

Rasha ta yi ikirarin cewa mayakan Azovstal na Ukraine 771 sun mika wuya a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, wanda ya kawo jimillar wadanda suka ajiye makaman tun ranar Litinin din wannan mako zuwa fiye da 1,700. Amma Shugaba Volodymyr Zelenskyy ya ce, Ukraine ta kuduri aniyar kwato yankunan kudancin kasar da sojojin Rasha suka mamaye.