Sojan Najeriya sun yi nasara | Labarai | DW | 02.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojan Najeriya sun yi nasara

Rundunar sojan saman Najeriya ta yi nasarar ragargaza wasu gungun mayakan Boko Haram da suka shirya kai farmaki a kauyen Bita a jihar Borno

A cewar rundunar sojojin saman Najeriya, sun datse 'yan ta'addan kan hanya kafin su kai ga isa kauyen na Bita, amma sun yi hakanne bisa taimakon sojojin kasa da ke basu bayanai. Wannan ruguza 'yan ta'addan ya zo ne kwana guda, bayan ziyarar da shugaban Najeriya ya kai jamhuriyar Benin, a woni shirin hada rundunar sojojin makobta da za ta ga bayan ta'addancin Bioko Haram. Tuni dai jamhuriyar Benin ta yi alkawarin tura sojojin kimanin 800 a cikin rundunar sojoji dubu 8.700 da ake son kafawa, bisa hadakar kasashe Najeriya, Nijar, Chadi, Kamarun da Benin.