1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar majalisun Jamhuriyar Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
June 23, 2017

A Jamhuriyar Nijar batun bai wa 'yan majalisun kasar kwangila na haifar da mahawara daga bangarori da dama ganin yadda ake zargin wasu shafaffu da mai daga 'yan majalisar da ke karbar kwangila duk da hanni kan hakan.

https://p.dw.com/p/2fGGt
Sitzung des Parlaments in Niger
Hoto: DW/M. Kanta

Tuni dai wasu yan rajin kare demokuradiyya suka lashi takobin yin fito-na-fito da yan majalisun da ke wannan dabi'ar. Sai dai a nasu bangaren 'yan majalisun sun ce mayar da su saniyar ware wajen samun hada-hada tamkar wani take hakkinsu ne. Irin gardamar da ta ke kaurewa kenan sau tari idan wani dan majalisar dokokin Nijar musamman ma wadanda aka san shi da jimawa da yin kasuwanci suka hadu da 'yan farar hula da ke hankoron kare demokuradiyya biyo bayan kamarin kace-nacen da ya kunno kai a baya-bayan nan na batun bai wa 'yan majalisun dokoki damar hada-hadar kasuwanci ko yin kwangila da gwamnatin kasar.

Kundin tsarin mulkin Nijar ne dai mai lamba 52 ya tabbatar da hana bai wa 'yan majalisun kwangila baya ga wasu masu mukamai na gwamnati kamar Shugaban kasa da Shugaban Majalisa ko Firaminista da sauran ministocin gwamnatin kasar. Sai dai wani abin cikas da kungiyoyin farar hula suka lura da shi a baya-bayan nan shi ne wasu shafaffu da mai na amfani da matsayinsu na siyasa a majalisar don karya dokar. Alhaji Nouhou Mahamadou Arzika, shugaban wasu kungiyoyin farar hula ne na MPCR ya ce 'yan majalisun da ke dabi'ar sun saba wa doka.

''Ba a barin dan majalisa ya yi kasuwanci, to amma yanzu gashi nan suna yi suna ta murde-murde, suna gama baki da ma'aikatansu na majalisa kasa-kasa suke yi. Dubi shi dan majalisa, doka ta ce baya iya shiga gaban wani don ya sami kwangila ko kuma ya shiga ya yi kwangila, amma ga shi nan suna yi. zance ne na doka akwai yanzu wanda doka ta hana shi ma shiga siyasa, kenan idan har dan majalisa na son kasuwanci da gwamnati to ya fita harkar majalisa''

Sitzung der Nationalversammlung in Niamey Niger
Hoto: DW
Niger Niamey Opposition
Hoto: DW/M. Kanta

Sai dai a na su bangare 'yan majalisun dokokin sun koka da rashin yin hada-hadar da suka ce ke taimaka masu wajen tafiyar da al'amuransu na siyasa, suna mai cewar ko baya gare su, dokar ta kawo nakasu wajen bunkasar harkokin kasuwanci ga matalauciyar kasar da kasuwancinta bai taka kara ya karya ba. Onorabul Algabit Alhaji Atta, dan majalisar dokokin Jam'iyyar PNDS tarayya mai ya ce:

''Dan majalisa da zarar ya zo nan ba abin da yake face sa hannu a kan doka, keta ce wannan irin ta su Nouhou, kuma wannan duk duniya babu shi in banda Nijar. Kai kana dan kasa amma an cimaka hakki.

A shekarar 2010 ne dai wata kwarya-kwaryar majalisa mai suna Conseil Consultatif Nationale lokacin mulkin rikon kwarya, ta kakaba ayar dokar bisa la'akari da kamarin lamarin da 'yan farar hula suka ce sun lura abin na yi a wancan lokaci. Sai dai wasu 'yan majalisun a yanzu sun ce ba abin da dokar ta tsinana face bakin ciki da bacin rai.